Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tillerson Ya Isa Moscow Domin Neman Hadin Kan Putin Kan Syria


Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson yayin da ya sauka a Moscow
Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson yayin da ya sauka a Moscow

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya isa birnin Moscow a yau Talata a wani mataki na kokarin shawo kan Rasha ta katse bai wa shugaban Syria Bashar al Assad kariya.

Ministocin kasashen da suka fi yawan masana’antu a duniya na G-7 sun gaza cimma matsaya a taron da suka yi a birnin Lucca na kasar Italiya a yau Talata, dangane da takunkumin da za a kakaba wa Rasha da dakarun Syria.

Ministocin sun dauki matsayar cewa ya kamata a fara gudanar da bincike kan wanda ya yi amfani da makami mai guba akan fararen hula a Syria a makon da ya gabata kafin a dauki wani mataki.

“Ba za mu sake barin hakan ta faru ba.” Tillerson ya fada wa manema labarai yayin da yake shirin kama hanyarsa ta zuwa Moscow inda ya kara da cewa “muna so mu kawo karshen wahalar da al’umar Syria ke fuskanta, kuma Rasha na da muhimmiyar rawar da za ta taka.”

Shugaban Amurka Donald Trump da Firai ministar Biritaniya, Theresa May, sun amince cewa akwai bukatar a matsantawa shugaban Rasha Vladimir Putin kan ya guje wa Assad saboda amfani da makami mai guba da ya yi.

Sai dai Jamus da Italiya, wadanda masu fada a ji a kungiyar kasashen ta G-7, sun hau kujerar na-ki.

“Kada mu kure (Vladimir Putin).” Ministan harkokin wajen Italiya, Angelino Alfano ya fada a yau Talata.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG