Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Watsi Da Ikirarin Rasha Kan Iskar Guba


Amurka ta yi watsi da ikirarin Rasha cewa, gubar iskar nan da ta yi sanadin mace-mace mai yawa a Siriya makon jiya, ta fashe ne a ma'adanar makaman 'yan tawayen Siriya inda aka boye ta, bayan da aka kai harin jirgin sama. Wani rahoton Amurka ya nuna cewa lashakka wannan gubar iska da niyya aka bada ta kan farar hula.

Majalisar Tsaron Kasa ta fito da wani rahoto a Fadar Shugaban Amurka ta White House jiya Talata mai bayyana cewa amfani da haramtaccen guba a matsayin makami da Siriya ke yi, wata barazana ce muraran ga duniya. Rahoton ya zargi Siriya da Rasha da neman yaudarar duniya game da wanda ya kai harin makamin guba kan mutane Siriya a wannan karon da kuma lokutan da su ka gabata.

Majalisar Tsaron Kasar ta yi kira ga al'ummar duniya da ta fito ta yi magana baro-baro ta kuma nuna karara cewa ba za a lamunta da wannan aika-aikar ba, kodayake Majalisar Tsaron ba ta bayyana abin da ka iya biyo baya ba.

A MDD, Amurka da Burtaniya da Faransa na kokarin komawa kan wani kuduri na da a yau dinnan Laraba - kodayake dai wannan hanzari da kyar ya kai labari saboda ana kyautata zaton Rasha za ta hau kujerar na ki game da batun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG