Shirin tantancewa zai zakulo jami'an da suka yi fice ta hanyar kara karatu mai shaidar digiri ko kuma difloma.
Muhammad K. Muhammad kwamishanan 'yansandan jihar Bauchi yace a duk rundunonin 'yansandan Najeriya gaba daya an bada umurnin a tantance jami'ansu. Na daya a tabbatar dansandan da yake neman mukami na gaba ya yi karatu. Na biyu kuma a tabbatar dansandan ya samu iziz nin yin karatun. Na uku a tabbatar hanyar gaskiya dansandan ya bi ya yi karatun ba wani ne yayi masa ba.
Wadanda wannan shirin ya shafa su ne masu neman zama sifeto ko mataimakin sufirtanda na 'yansanda wato ASP a takaice. Duk wanda yake neman ya zama sifeto dole ya kasance yana da takardar shaidar kammala karatun sakandare tare da cin akalla fannoni biyar da suka hada da turanci da lissafi. Ya kamata kuma yana da difloma ko karatun NCE.
Wanda yake neman mukamin ASP to dole ne yana da digiri ko HND, wato difloma mafi daraja ta Polytechnic. Wadanda basu da ilimin da ake bukata ba zasu iya cigaba ba a aikin 'yansandan yanzu na kasar.
Su ma jami'an 'yansandan sun furta albarkacin bakinsu dangane da wannan sabon shirin. Wata da tayi shekara shida a aikin 'yansandan tana neman mukamin sifeto domin tana da karamar difloma kamar yadda sabon shirin ya bukata. Tace shirin zai taimaka masu a aikinsu domin babu yadda mutum da bai iya karatu da rubutu ba zai iya aikin.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5