Wadannan kalaman sun fito ne lokacin da babban hafsan mayakan Najeriya Lt.Col. Kanneth Minimah, wanda ke kaddamar da karamar cibiyar yaki da ta’addanci a Yola fadar jihar Adamawa domin ta taimakawa shedikwatar garin Maiduguri.
A mayar da martani kan rahotan da Amnesty International ta fitar Kanneth Minimah yace, “idan ka tsaya ka nazarci abin zakaga abin a kwai munafunci da sharri kuma wani abu ne akayi don a kawo kutungwila ga yaki da ta’addanci, ba yau kawai suka fara ba sun dauko tsoho labari suka yi mishi kwaskwarima da hadawa da sunana wasu hafsoshi da suna aiki yanzu wasu kuma sunyi murabus.”
Idan za’a iya tunawa ranar ashirin da tara ga watan Mayu, Shugaba Muhammadu Buhari, yayi umarni ga askarawan Najeriya da su maida hedikwatar cibiyar yaki da ta’addanci zuwa jihar Borno a wani mataki na dakushe hare-haren da kungiyar Boko Haram ta share sama da shekaru shida tana kaiwa mazauna kudu maso gabashin Najeriya.
Kwanaki biyu da suka gabata ne babban hafsan soja Lt.Col. Kanneth Minimah, ya cika wannan umarni na shugaban kasa inda ya kaddamar da cibiyar yaki da ta’addanci a jihar Borno, yakuma ziyarci garuruwan Bulka da Goza, alokacin wannan ziyara da babban hafsan sojan ya kai Yola ya shaidawa manema labaru cewa yaje Yola ne domin kafa karamar cibiya wadda zata rika taimakawa babbar cibiyar yakin da ta’addanci da aka kafa a garin Maiduguri mai lakabi da “Operation Zaman Lafiya” hakan zai rage gibi da ake da shin a sadarwa harma da nisan da ke tsakanin cibiyar da babbar hedikwatarta dake garin Abuja.