Wakilin Sashen Hausa dake jihar Borno Haruna Dauda Biu ya tattauna da shugaban rundunar sojan Najeriya dake Borno
‘’Kamar yadda shugaban kasa yace a ranar da ya karbi mulki ranar 29 ga watan mayu da ya wuce yace a kirkiro ko kumna a matsar da hedikwatar ta rundunar sojoji a Maiduguri yadda za a taimaka kuma a tallafa wa fadan da ake yi da taaddanci to wannan umurni an karbe shi hannu bibbiyu wannan umurni da aka bada yanzu an aiwatar dashi don haka muna nan Maiduguri kuma nan bada wani dan lokaci ba hatta su kansu hafsan hafsoshi zasu rika aiki nan Maiduguri, abinda nake son mutane su gane shine musammam wadanda suka san aikin soja ba wai ana son a musuna wa aikin bane a’a taimaka mashi za ayi don haka duk wasu abubuwa da ake bukata maimakon a nufi Abuja ko wani abu tunda tana nan Maiduguri nan da nan zaka ga an taimaka kuma kasan shaanin soja kome ake yi ana yi ana rubanya wa, baya ga wannan Hedikwata da take nan Maiduguri muna da abinda ake kira da turanci Alternate Headquarter a Yola dake jihar Adamawa’’
To ranka ya dade kamar kunshirya Kenan domin kawo karshen wannan taadanci dake faruwa a wannan shiyya?
‘’Kusan kullun ai dama cikin wannan shiri muke kai da kake zaune nan Maiduguri kafi kowa sani’’
Yanzu wani tabbaci zaku baiwa alummar Maiduguri cewa dawowar ku nan ba zai zama matsala ba ga al’ummar Maiduri musammam ganin cewa yawancin jamiaan ku cikin gari suke.
‘’Ko alama ba wata matsala da zata jawo saima kara habbaka dangantaka dake tsakanin sojoji da al’ummar gari ba don kome ba domi su kansu mutanen gari sunyi Imani cewa sojojin sunzo nan ne domin su sadaukar da kansu domin kawo zaman lafiya daci gaba kaga mutumin da ya kawo maka douki yaushe za a zo ana samun sabani ko da yake ance zamu zauna zo mu saba ai sojoji koda wani lokacii suna da kaidojin aiki kuma duk wanda yayi ba abinda shike nan za a bincike shi a tuhume shi a zartas masa da hukunci kamar yadda ya kamata, sai dai abinda nake son nayi anfani da wannan damar in fadawa mutane cewa muna nan ne ba domin kome ba sai don kawo karshen wannan taadancin da ya addabi al’ummar mu gaba daya, don haka muna bukatar hadin kai addua da kuma duk wanda yake da wani bayani a inda wadannan yan taada suke to ya samu jamiaan tsaro ya fada musu, domin ance hannu daya baya daukar jinka’’.
Ranka ya dade a yan kwanakin nan akwai wau jamiaan ku da yan kwanakin nan sukan bi wasu su damke su da ake tuhumar sojojin bente ne shin wai meke faruwa ne?
‘’To yanzu ne nake jin wannan bayani koda yake naso da ka fayyace kome kake nufi, domin duk loacin da aka samu al’amari kamar haka wasu sukan yi anfani da wannan damar domin su cuci al’umma ko su musguna musu ba tare da kaidar aiki ba a kullun don haka muke idan ka duba bayan ka akwai wani Kanar gaya can baya ka ganshi da wani tambari da aka nuna aka ce MP wadannan sune yan sandar sojoji sune aikin su tsawata aikin da soja suke yi yana kan kaida’’.