Sanadiyar harin da 'yan fashin suka kai an ce sun sace makudan kudi tare da tserewa ba tare da an kamasu ba.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa 'yan fashin da suka hada da wata mace sun ta harba bindiga sama tare da tsorata al'ummar dake anguwar.
Bayan fashin an bayyana cewa 'yan fashin sun tsere ta jirgin ruwa tare da kona wasu motoci uku da suka zo dasu.
Wasu da suka shaida lamarin sun ce 'yansanda sun kawo doki tare da musayar harbe-harbe tsakaninsu da 'yan fashin. Amma 'yansandan ba su yi nasarar kama ko kashe daya daga cikin 'yan fashin ba.
Daga bisani kwamishanan 'yansandan jihar Legas Mr. Kayode Aderanti ya ziyarci inda lamarin ya auku. Ya sha alwashin cewa 'yansandan zasu gano 'yan fashin tare da tabbatar da cewa za'a gurfanar dasu gaban kuliya da zara an kamasu.
Kazalika kakakin rundunar 'yansandan Mr. Ken Nwosu yace rundunar zata bada tukuicin nera miliyan biyar ga duk wanda ya bada labarin da ya kaiga samun cafke 'yan fashin.
Ga rahoton Babangida Jibrin.