An samu yamutsi da hargitsin matafiya akan titin zuwa Kaduna daga Zaria biyo bayan harbe wani matukin mota da sojoji suka yi saboda bai basu iyakacin kudin da suka bukata a hannusa ba.
Matafiyan sun yi korafi akan abun da sojojin suka yi suna cewa sojojin ma basu da hurumin tsaresu ko neman na goro a hannun direban. Sojan ya nemi matukin motar ya bashi nera dari biyu ne amma ya bashi nera dari daya lamarin da ya sa sojan ya hasala ya kuma harbi matukin a kafa .
Matuka manyan motoci da suka fusata sun datse hanyoyin shiga da fita garin Kaduna daga hanyar Zaria tun daga misalin karfe goma sha daya na dare har zuwa karfe daya na Litinin. Matukan sun ce mabudin bude hanyoyin shi ne fada masu bahasin harbe dan'uwansu da sojin ya yi. Bugu da kari sun ce ai kudin da sojoji ke karba hannunsu cikin dare haramun ne.
Matukan da abun ya faru a idanunsu sun yi karin haske. Sun ce suna zuwa sai suka ga sojojin sun gayawa direban ya sauko, yana sauka kuma suka harbeshi akan ya rena nera dari daya da aka bashi maimakon dari biyu. Sun ce duk wanda ya biyo hanya sai ya tanadi kudin da zai bayar, kudin cin hanci da ya zama tamkar dole.
An bude hanyoyin ne bayan da masu ruwa da tsaki suka amince su yi zama na musamman akan lamarin. Sojojin da suka aikata wannan danyan aikin an kamasu kuma suna tsare. Matukan sun ce zasu bukaci a cire duk wani soja daga hanya. Basa bukatansu.
Ga karin bayani.