Sabuwar Dokar Hana Kiwo a Jihar Lagos

Unguwar Oyingbo a jihar Legas (Reuters)

Gwamnatin jihar Lagos ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a jihar sakamakon wata doka da gwamnan jihar Mr Babajide Sanwo Olu ya rattawabawa hannu.

Dokar ta tanadi daurin shekaru uku zuwa sama ga laifukan dake da alaka da kiwo a jihar. Kwanaki 11 kenan tun amincewa da wannan doka da Majalisar jiha ta yi.

Samar da wannan doka na nufin babu kiwo baki daya a fadin jihar Lagos, lamarin da ya biyo bayan wasu taruka masu yawa da gwamnonin Kudancin Najeriya suka yi, inda suka cimma matsayar hana kiwo domin samar da zaman lafiya a yankin.

An jima ana zargin Fulani makiyaya da yawan kai hare-hare har ma da fada tsakaninsu da manoma.

A daya bangaren kuma, shugabannin kungiyoyin Fulani na Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu game da dokokin da gwamnonin yammacin Najeriya ke kafawa, wanda suka ce dokokin ba sa bisa kudin tsarin mulkin kasa.

Shugaban al’ummar Fulani na Shagamu Alhaji Salisu Garba, ya ce abin tsoro anan shine idan har Yarabawa suka fara kaiwa Fulani hari daga nan lamarin zai iya shafar kowane dan Arewa kan cewa duk Fulani ne.

Muryar Amurka ta ji ra’ayoyin wasu mazauna Lagos game da wadannan dokoki da aka kafa, sai dai yawancin ra’ayoyin sun nuna rashin jin dadi game da dokokin.

Matakin da ake gani ya sabawa dokokin Najeriya da na kasa da kasa, don tsarin mulki ya baiwa kowane dan Najeriya damar shiga da zama a duk inda yake so a fadin kasar.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabuwar Dokar Hana Kiwo a Jihar Lagos - 3'10"