Kungiyar ta cimma matsayar ce a jihar Legas da ke kudancin kasar, inda taron ya amince birnin ya zama hedkwatar kungiyar gwamnonin yankin daga yanzu.
Ga wasu daga cikin manyan batutuwa da kungiyar ta amince da su kamar yadda wata sanarwa da shugabanta gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Odunayo Akeredolu ya sa hannu akai ta nuna:
- Kungiyar ta nemi a rika tsarin mulkin karba-karba kan shugabancin kasar.
- Ta jaddada cewa, kudu za a ba damar ya shugabanci Najeriya a 2023.
- Taron ya yabawa jami’an tsaro kan namijin kokarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya tare da jajintawa iyalan jami’an tsaron kasar da suka rasa ‘yan uwansu.
- Jaddada bukatar a samar da ‘yan sandan jiha.
- Taron nasu ya amince cewa, a duk lokacin da jami’an tsaro za su kai wani samame a wata jiha, dole a rika sanar da babban mai tsaron jihar (gwamna).
Karin bayani akan: Nigeria, da Najeriya.
- Ba ta bai gamsu da yadda ake nuna son kai wajen aiwatar da hukunci ba sannan ya nuna cewa a duk lokacin da za a kama wanda ake zargi da laifi, a yi hakan bisa tsarin doka da tabbatar da an kare ‘yancin bil adama.
- Taron gwamnonin na kudancin kasar, har ila yau, ya amince cewa ranar Laraba 1 ga watan Satumba, 2021 dokar haramta kiwo a fili za ta fara aiki a duk jihohin yankin kudancin kasar.
- Gwamnonin yankin ba su amince da kaso 3 da za a rika ba jihohin da ake tono arzikin mai ba, amma suna goyon bayan kashi 5 kamar yadda majalisar wakilai ta ba da shawara.