Kimanin alhazai 2000 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsutsun da ya faru lokacin aikin hajjin bara, kuma kimanin kashi Goma na Alhazan ‘yan Najeriya ne. Domin kucewa sake faruwar hakan yasa ma’aikatar aikin Hajji ta Saudiyya ta tsara yadda za ayi jifan Shedan daki daki. Inda aka shirya Alhazan kowacce ‘kasa zasuyi nasu daban daban, maimakon yi tare kamar yadda aka saba a baya.
Shugaban aikace aikace na hukumar Alhazan Najeriya da ke birnin Makkah Dakta Aliyu Tanko ya yiwa wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina ‘karin bayani, inda yake cewa cunkoson da ake yi na lokaci ‘daya daga cikin dalilan da zai sa a sake samun hadarin da ya faru bara, shiyasa yanzu aka dauki matakai inda aka fitar da jadawali ga kowacce ‘kasa na lokacin da zasu fara nasu jifan Shedan din.
Wasu daga cikin Alhazan Najeriya sun yabawa wannan matakai da tsarin da aka dauka domin dakile afkuwar hadarin bara.
Mahukuntan daular Saudiyya sun tsara yin amfani da kimiyyar zamani don tsaurara matakan tsaro, wanda masu sharshi ke ganin hakan baya rasa nasaba da aikace aikacen ‘yan ta’adda ya yawaita a kasashen larabawa. Kakakin ma’aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya Manjo Janar Mansur Turki, yace wannan sabon tsarin shine muhimmin shirye shirye a aikin hajji bana. Yanzu dai birnin Makkah ya ‘dauki harami, inda Alhazai daga sassa daban daban na Duniya ke ta shirye shiryen fara aikin Hajji gadan gadan.
Saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5