‘Yan Shi’a dai maza da mata sunyi maci tsakiyar Abuja da yekuwar neman sakin shugaban na su dake adane tun watan Disambar bara, bayan arangamar sojoji da da ‘yan Shi’a a Zariya.
‘Yar shugaban kungiyar Shi’ar Suhaila Ibrahim El-Zakzaky da tace ta samu ganin mahaifin nata ta yi ‘karin bayani. Inda tace yanzu haka duk da cewa kafarsa na samun ‘dan sauki amma da rauni a tare da shi, domin hannunsa bai gama warkewa ba. ta kuma ‘kara da cewa yanzu haka ya rasa wani bangare na jikinsa Idanunsa.
Kama daga kwamitin bincike na gwamnatin Kaduna wanda ya kammala aiki ya mika rahotansa kan akasin, har zuwa hukumar kare hakkokin bani Adama sun saurari bayanai daga dukkan sassa dake alaka da arangamar da bada tabbacin yin adalci.
Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Kaduna ya bada tabbacin bin kadun dukkan sassan, baya ga batun na ‘yan Shi’a El-Rufa’i ya bukaci Malaman Islama su dage wajen shiga yankunan karkara don wayar da kan musulmi akidun Islama don rigakafin duk wani lamarin da ka iya tayar da husuma nan gaba.
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.