Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Makamai A Hannun Jama’a Shine Ke Haifar Da ‘Karuwar Ayyukan Ta’addanci


NIGER: Taron horas da jami'an tsaro akan makamai 2
NIGER: Taron horas da jami'an tsaro akan makamai 2

Ayyukan masu satar mutane domin neman kudin fansa na ‘kara ‘karuwa a jihar Taraba dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

Lamarin da ya kai har a Jalingo fadar jihar Taraba, al’umma basu tsira ba kamar yadda ya faru a bakin bankin Zenith inda akayi awon gaba da wani matashi mai kimanin shekaru 28 da haihuwa. Ko da yake daga karshe an tsince shi ne a wani ‘kauye dake kusa da garin Numan a jihar Adamawa.

Bincike dai na nuni da cewa yawan makamai a hannun jama’a shine ya harfar da yawaitar ayyukan ta’addanci kama daga Boko Haram da sace mutane da kuma ayyukan tsageranci a yankin Niger Delta dake da albarkatun Mai a Najeriya.

Wadannan matsaloli ne yasa yanzu ake samun karuwar kungiyoyin sa kai na ‘yan Banga, domin su kaiwa al’umma ‘dauki da kuma taimakawa jami’an tsaro to sai dai kuma tuni yanzu ne ma aka fara kokawa game da wasu kungiyoyin da suka hada da na wani mai yaki da bata gari a jihar Taraba da ake yiwa lakabi da Shehu Musa Aljan, batun da yasa rundunar ‘yan Sandan jihar fara bincike kan ire iren ‘yan aikin sa kan.

Da yawa dai akan zargi irin wadannan kungiyoyin sa kan ne da wuce makadi da rawa wajen yankewa wanda ake zargi hukunci ta hanyar ‘dauri da ma sauran nau’o’in azabtarwa.

Saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG