Muryar Amurka ta zanta da Sanata Suleiman Nazif mai wakiltar arewacin Bauchi akan takaddar siyasa da ta shiga tsakaninsu 'yan majalisun tarayya daga jihar da gwamnan jihar su.
'Yan majalisun ta bakin Sanata Suleiman Nazif suna neman gwamnan ya basu amsa ne akan abubuwa goma sha daya da suka hada da zargin karkata kudin tsaro da kudin tallafawa matasa da dai sauransu. Yace kawo yanzu gwamnan ya bada amsa ne akan abu daya tak.
Yace ba zata yiwu a ce ana siyasa gwamna na kan gabansa. Kamata ya yi a tafi tare domin a rayu tare. Bai kamata a ce an samu kace-nace ba a cikin shekara daya da tafiya.
Inji Sanata Nazif yace an ce yara na gudu daga makarantu saboda babu abinci. Ana musgunawa sarakuna. Ana cire hakimai ba bisa kaida ba. Alatilas ne a duba abubuwan tare a kawo masalaha. Gwamna ya gane cewa jam'iyyar APC daban, gwamnan jihar Bauchi kuma daban yake.
'Yan majalisun na zargin gwamnan da fada masu wani abu daban amma sai ya juya ya aiwatar da wani abun daban.
Ga cikakken firar da Medina Dauda domin karin bayani.