A ci gaba da neman hanyoyin zaman lafiya a tsakanin al’umomin dake gabada juna a jahar Filato, kwamitin da majalisar dokokin jahar ta kafa dan gano musabbabin rikicin da bada shawarwari kan matakan da za’a dauka.
A karon farko ya hado kan dukkan sarakuna gargajiya dake kananan hukumomin Barikin Ladi,da wasu bangaren Mangu da jami’an tsaro.
A zaman tattaunawar da sukayi dukkani al’umomin sun bayyana rashin jindadin su da taske tashen hankulan dake kai rasa dinbin rayuka da dukiyoyi.
Dagwon Rei, na Barikin Ladi Edward Buot, ya ce irin wannan taron nada mahimmanci domin inda kowa yayi maga daga nan sa’a gano bakin zaren har a samun mafitar babu wanda bai son a zauna lafiya da Fulani kamar yadda ake da can.
Shima Umaru Baba, Ardon, Langai daga karamar hukumar Mangu, ya bayyana cewa barin kowa ya koma wurin san a assali zai taimaka wajen samun zaman lafiya.
Kwamandan rundunar tabbatar da tsaro a jahar Filato, Brigediya Janar M H Madaki, ya bukaci al’umomin ne dasu dunga fadin gaskiya dan yiwa kansu adalci, ya ce rundunar tsaro da STF, ba zata yi amfani da karfi wajen kawo zaman lafiya ba sai in ku jama’a ku rugumi zaman lafiyar da kan ku.
Shugaban kwamitin kuma mataimakin kakakin majalisar dokokin jahar Filato Yusuf Adamu Gardi, ya ce kamata yayi Gwamnatin tarayya ta karo jami’an tsaro kamar yadda tayi a arewa maso gabashin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5