Yayin da Majalisar Dattawan Najeriya ke cigaba da tantance sunayen wasu ‘yan Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar don zama Ministocinsa, Shugaban ya gabatar da kashi na biyu na sunayen wadanda Majalisar za ta tantance don zama Ministoci. Mutane 16 da Shugaba Buhari ya gabatar da sunayensu jiya sun hada da Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim (daga jahar Yobe); da Claudius Omoyele Daramola (jahar Ondo); da furfesa Anthony Anwuka (jahar Imo).
Sauran sun hada da Jeffrey Onjema; da Birgediya Mansur Dan Ali; da James E Ocholi, SAN (jahar Kogi); da Zainab Shamsuna Ahmed; da Okechukwu Enelamah; da Barrister Muhammadu Bello (jahar Adamawa); da Aisha Abubakar; da Sanata Heineken Lokpobiri (jahar Bayelsa); da Adamu Adamu (jahar Bauchi) da furfesa Isaac Adewole; da Pastor Osani-Osani Oguro; da Honorabul Abubakar Bawa Bwari.
A halin da ake ciki kuma, an fara tantance sunayen da aka gabatar tun makon jiya. To saidai an karyata cewa da ake sai Sanatoci a kalla biyu daga jahar da mutum ya fito sun amince kafin a wanke shi. Sanata Shola Adeyeye Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawa ya gaya ma Madina Dauda cewa sun tattauna a Majalisar amma babu inda aka taba ba da wannan sharadin.
Yanzu adadin mutanen da za a tantance don zama ministoci sun kai talatin da bakwai Kenan. Ga Madina Dauda da cikakken rahoton: