Ita ma Amurka a jiyan,ta jefa kimanin ton hamsin na kananan makamai wa ‘yan tawayen Syria ta jiragen sama a arewacin kasar.
A fada mafi tsanani da aka gwabza a ‘yan makonnin nan, sojojin gwamnati suna ta yakar ‘yan tawayen a wasu muhimman wurare a tsakiyar yankin Hama, da nufin sake kwato ikon kan yankin da ake kira Sahl al-Ghab.
Amma 'yan gwagwarmaya suna ikirarin cewa 'yan tawaye sun takawa farmakin dakarun gwamnatin birki. Sannan kungiyar lura da hakkin bil’adama ta Syria ta bada rahoton cewa an zafafa gumurzun da ake yi tun lokacin da Rasha ta kaddamar da hare hare cikin kasar a karshen watan Satumba.
Rasha tace jiragen yakinta sun fatattaki cibiyoyi ko muradun 'yan tawaye guda 53 a Syria a cikin sa’o’i 24 a yankunan Hama, Homes, Latakia da Idlib. A yayin da suma sojojin da Amurka ke jagoranta ke ci gaba da ragargaza sansanonin ‘yan ISIS.
Musamman a kusa da Al-Hasaka da Washiya sojojin tarojn dangi sun kai hare hare goma sha takwas ta sama a Iraqikusa da garuruwan Bayji, Fallujah da Mosul, kamar yadda cibiyar kula da harkokin yaki na mayakan Amurka ta sanar.