Rundunar Sojojin Najeriya Ta Fadakar da Mutane Akan Kaucewa Shiga Ta'adanci

Janar Burutai hafsan hafsoshin sojojin Najeriya

A makon da ya gabata ne rundunara sojojin Najeriya ta gudanar da wani taron fadakaewa ga wasu 'yan gudun hijira da kuma wasu da sojojin ke rike dasu.

Manufar fadakarwar itace dora mutanen kan hanyoyin da suka dace kada su fada hannun wadanda ka iya karkatasu zuwa shiga aikin ta'addanci.

Taron ya samo asali ne daga Abuja zuwa wasu jihohi dake arewa maso gabashin Najeriya musamman jihohin da suka samu kansu cikin tashin tshina.

Kanar Umar Musa Aliyu shi ya jagoranci taron fadakarwan.

Bayan taron na mako guda Kanar Aliyu ya yiwa Muryar Amurka bayanin manufar taron. Manufar ita ce a fadakar da wadanda suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira saboda su sojoji su samu su gudanar da ayyukan da dokar kasa ta rataya masu.

Su 'yan gudun hijiran sun yi alkawari cewa duk inda suka shiga zasu zama 'yan kasa nagari saidai a cigaba da addu'ar samun zaman lafiya.

Kanal Bawa Salisu na cikin manyan sojojin da suka yi jawabi. Yace sun yi masu bayani akan addinin musulunci da yadda yake muamala da wadanda ba musulmai ba. Yace akwai rashin fahimta da dama wadda ta haddasa rigingimun da ake fama dasu. Abun da 'yan Boko Haram suke yi ba musulunci ba ne. Kada a alakanta dabi'un 'yan Boko Haram da musulunci

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Fadakar da Mutane Akan Kaucewa Shiga Ta'adanci - 4' 51"