Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram Ta Sake Kai Hari a Jihar Adamawa


Mazauna kauyukan Adamawa na tserewa daga Boko Haram.
Mazauna kauyukan Adamawa na tserewa daga Boko Haram.

Kauyukan karamar hukumar Madagali dake arewacin jihar Adamawa suna yawan samun hari daga 'yan Boko Haram dake farmasu cikin tsakar dare.

Wasu 'yan bindigan da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a kauyen Kubla cikin karamar hukumar Madagali.

Har yanzu ba'a san adadin wadanda wannan sabon harin ya shafa ba domin a cikin dare aka kai harin .

Banda harbe mutane 'yan bindigan sun kona gidaje duk da cewa tazarar dake tsakanin Kubla da inda sojoji suke bai wuce kilomita uku ba.. Sun kone gidajen kauyen lamarin da ya sa wadanda suka tsira sun fice ne a firgice.

Inji wani ganao inda 'yan Boko Haram din suka ja daga kimanin kilomita biyar ne daga Kubla a wani kauye da ake kira Galta. 'Yan bindigan suna zuwa ne da kekuna.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Michika da Madagali Adamu Kamale ya tabbatar da sabon harin da aka kai. Yace kowacce rana ko wane lokaci ana shiga Madagali ana kashe-kashe. Yace an dannesu ana kashesu amma basu ga sojojin Najeriya ba. Yace a fito a fadi gaskiya.

Adamu Kamale ya yi zargin rashin kula da yankin nasu daga hukumomin jiha da na tarayya.

To saidai gwamnan jihar Adamawa Muhammad Bindoji yace suna daukan mataki tare da hadin kan sojoji.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG