Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Zasu Rushe duk Gidan da Aka Yi Anfani Dashi Wajen Ta'adanci


Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai
Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

Manjo Janar Yushau Abubakar kwamandan sojojin dake yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya bayyana abubuwan da suka faru game da bamabaman da suka fashe a birnin Maiduguri

Kwamandan yace yanzu sun tabbatar cewa abubuwan da suka gano su ne aka yi anfani dasu wajen hada bamabaman to amma basu tashi ba. Suna bincike..

Dole ne sojoji su rike bamabaman da basu tashi ba domin a tabbara da inda suka fito da zummar zakulo wadanda suka sarafasu.

Kwamandan yace akwai matakai da yawa da suke dauka dangane da kare rayukan mutane.

Kwamandan ya jawo hankalin jama'a akan cewa zaman lafiya ya rataya akan kowa saboda a duk fadin duniya babu inda za'a samu jamai'an tsaro a kowane lungu.

Yakamata jama'a su gane cewa kowa dansanda ne a anguwarsa, wato ta hanyar kare tsaro inda mutum yake. A kowane lokaci kowa ya san abun dake faruwa a anguwarsa. Duk abun da ya shigo anguwa da ba'a gane ba to kamata ya yi a shaidawa jamai'an tsaro.

Kwamandan yace akwai wata kwamiti da hafsan hafsoshin kasar ya kafa wadda ta kunshi kwararru dake iya tantance mutane su san mugu da nagari daga cikinsu. Akwai irin wadannan kwararrun kusan tamanin da suke aiki da rundunar sojin kafada da kafada.

Wani abu sabo da sojojin suka fito dashi shi ne kudurin rushe kowane gida aka yi anfani dashi wurin sarafa bamabamai ko daurawa wata ko wani da zummar tayar da bam din.

Daga yanzu duk wanda ya bar gidansa 'yan ta'ada suka yi anfani dashi to ya kuka da kansa saboda sojoji zasu rusa gidan. Bugu da kari irin wannan mutumin sojojin zasu gurfanar dashi gaban shari'a.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG