Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bama Bamai Sun Tashi A Kuje Da Nyanya Duka A Kewayen Abuja


‘Yan kwana-kwana a wurin da Bom ya fashe a Abuja a bara.
‘Yan kwana-kwana a wurin da Bom ya fashe a Abuja a bara.

Fashe Fashen sun auku ne a kasuwar garin da kuma kusa da ofishin 'Yansanda.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda cewa harin da aka kai kusa da ofishin 'Yansanda na Kuje, wata mace ce ta kai harin kunar bakin wake. Sai dai Abdullahi Shu'aibu, yace harin bai taba ofishin 'Yansandan ba, babu wadanda wannan hari ya rutsa dasu in banda ita wacce ta kai harin.

Na biyu kuma, sai wanda aka kai a kasuwar Kuje, nan ma inji Abdullahi, anyi sa'a harin ba a ciki-cikin kasuwar bane, a bakin kofa ne, inda aka auna arziki, domin da rana ne aka kai wannan hari inji shi, motocin kasuwa suna yawan tsaye-tsaye a wurin.

Da aka tambayeshi ko yaga gawarwaki yace, a'a jami'an tsaro sun killace wuraren saboda haka hakikanin ko akwai wadanda harin ya rutsa dasu sai zuwa da safe.

Sai kuma a Nyanya, nan ma wani mazaunin garin ya gayawa wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda cewa, da misalin karfe 10 da 'yan kai ne suka ji karar wasu fashe fashe masu karfi, kuma nan da nan suka ji mutane suna kuka, da suka isa wurin babu kyawun gani.

Yace jami'an tsaro, da ma'aikatan kiwon lafiya da motocin daukar marasa laifya, suna ta kokarin jigilar wadanda suka jikkata

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG