Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Yi Bikin Cika Shekaru 54

Babban Hafsan sojojin saman Najeriya da Takwaransa na sojojin Ruwan Najeriya

Rundunar sojojin saman Najeriya na bukin cika shekaru 54 da kafuwa, tare da duba ire-iren nasarorin da rundunar ta cimma cikin wadannan shekarun.

Manyan Kwamandojin rundunar sojojin saman Najeriya sun hallara a birnin Kaduna, inda ake bikin cika shekaru 54 da kafa rundunar tare da tilawar irin nasarorin da aka cimma cikin wannan lokaci.

Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadik Abubakar, ya ce tun da aka kafa rundunar a shekarar 1964 zuwa yanzu rundunar ta sami nasarori masu tarin yawa, kuma tayi rawar gani tun lokacin yakin basasa da lokaci da ‘yan tawayen Chadi suka shigo Najeriya.

Haka kuma rundunar taimaka lokacin yakin Laberiya da Saliyo, inda ta tura jiragenta don kawo karshen yake-yaken.

Daya daga cikin tsofaffin jami’an rundunar Abubakar Umar Tsanni, ya bayyana irin gudunmawar da rundunar sojojin sama ta bayar don kawo zaman lafiya a rikicin cikin gida dake faruwa.

A lokacin bikin kimanin sama da jiragen yaki 25 ne suka gudanar da atisayen kayatar da manyan baki, wasu daga cikin sojin saman kuma su kayi saukar lema.

Sojan kundunbalanne wannan bayan ya sauka

​Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Yi Bikin Cika Shekaru 54 - 2'32"