Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya, China Za Su Musanya Dala Biliyan 2.5


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

A wata dabara ta kauce ma amfani da dalar Amurka kulluyaumin a lokacin hada-hadar cinakayya, kasashen China da Najeriya sun cimma yarjajjeniyar musanyar dalar Amurka da dama tsakaninsu.

Babban Bankin Najeriya da Bankin Al’umma na kasar China, sun cimma wata yarjajjeniya ta musayar takardun kudin da su ka kai dalar Amurka biliyan 2.5, saboda su rage dogaro ga dalar Amurka a yayin cinakayyarsu ta bai daya.

Gwamnan Babban Bakin Najeriya Godwin Emefiele ne ya jagoranci jami’an Najeriya, a yayin da shi kuma Gwamnan Bankin Al’umma na kasar China, Yi Gang, ya jagoranci tawagar China a hidimar rattaba hannu kan yarjajjeniyar a birnin Beijing a makon jiya.

Manufar wannan yarjejeniyar ita ce samar da isassun takardun kudaden hada-hada ga kamfanoni da masana’antun Najeriya da China da kuma rage wahalar da su kan fuskanta yayin neman takardun kudi na dabam.

Wannan yarjejeniyar, wacce ta musanyar takardun kudade ce kawai, za ta saukaka samun takardar kudi ta Naira ga ‘yan China masu masana’antu da ke bukatar sayo kayan sarrafawa daga Najeriya, ta yadda za su rika samun Nairar daga bankunan kasar China su biya kudaden kayan da su ka sayo.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG