Yace sun sami makaman harbo jirgin sama da albarusansu. Daga ciki, akwai kuma wata bindiga ta musamman da ake kira “General Purpose Machine Gun”, banda haka kuma, yace akwai wata bindiga da mafiya yawa masu amfani da ita, sune sojojin sama, da bindigogi masu sarrafa kansu kala kala.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma sami wayar salula da kuma SIM card guda uku wadanda za a bincika domin neman samun bayanai a cikinsu. Wakazalika rundunar sojin ta samo akwatuna na harsasai na musamman. Bisa ga bayaninsa, an lalata wadansu makaman a can saboda haka ba zasu dauku ba.
Kanar Tukur ya bayyana cewa babu wanda suka kama a samamen sai wadanda suka kashe, yayinda a nasu bangaren ba a kashe kowa ko raunata wani soja ba. Ya bayyana cewa, wannan ne karon farko da sojojin Najeriya suka shiga Dikwa.
Bisa ga cewar Kanar Tukur, a saninsu, babu ko karamar hukuma daya dake hannun kungiyar Boko Haram. Sai dai sun san cewa, wani lokaci sukan shigo suyi barna su saci kayan mutane, amma babu ko Karanar hukuma daya da za a ce gaba daya, wata karama tana hannun Boko Haram.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana
Your browser doesn’t support HTML5