Ana sa ran maniyyatan aikin hajjin su dubu daya da dari bakwai da talatin da biyu ne zasu tashi a jahar arewa ta kasar Ghana zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali.
Jirgin saman Nas Airline na kasar saudiyya ne ya kwashe rukunin farko na alhazan Ghana su dari hudu da biyar kamar yadda Alhaji Sumaila jigo a hukumar aikin hajjin kasar yayi wa muryar Amurka bayani.
Kafin maniyatan aikin hajji su tashi, Shugaban hukumar aikin Hajjin Sheikh IC ya bukaci maniyyatan su daukaka tutar kasar Ghana ta hanyar bin doka yayin sauke faralinsu a kasa mai tsarki.
Wasu maniyyatan da Muryar Amurka ta yi hira da su, sun bayyana farin ciki ganin yadda aka tsara shirin tantance maniyyatan aikin hajji kafin su tashi zuwa Saudiyya.
Ana sa ran maniyyatan aikin hajji sdubu daya da dari bakwai da talatin da biyu ne zasu tashi daga Tamale a jahar arewa kazalika dubu daya da dari uku da talatin da bakwai su tashi a filin tashi da saukan jiragen saman kasa da kasa ta Kotoka dake Accra. A kowace shekara Ghana na samun kujerun aikin Hajji fiye da dubu shidda amma bana adadin ya ragu sakamakon wasu matakan da hukumomi a Saudiyya suka dauka tun lokacin da cutar covid 19 ta zamo annoba.
Saurari cikakkne rahoton Hamza Adams cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5