Kasar Indonesia ta tura wata babbar jami'arta zuwa kasar Myanmar domin shiga tsakani a rikicin 'yan kabilar Rohingya da hukumomin jihar Rakhine.
Maksudin ziyarar ita ce domin su tattauna akan abinda ke faruwa a jihar Rakhine.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ’yan asalin jinsin Rohingya su dubu 87 ne suka gudu daga jihar zuwa makwabciyar kasar Bangaladesh tun lokacin da fada ya barke a farkon watan jiya.
Shugaban kasar na Indonesia Joko Wododo, ya ce Ministan tashi za ta bukaci gwamnatin kasar ta Burma da ta hana ci gaba da fadan da ke dalilin kashe mutane, kana daga nan kuma ta zarce zuwa kasar Bangaladesh domin tsara yadda za a taimakawa wadanda suka tsere suka shiga cikin kasar.
Fada na baya-bayan nan shine wanda aka fara a ranar 25 ga watan Agusta, sa'ilin da wasu ‘yan tsagerun Rohingya suka farma wani caji ofis da ma wani sansanin soja a kokarin su na kare ‘yan kabilarsu daga cin zarafin da ake musu.
Rundunar sojan kasar ta ce mutane 400 ne suka mutu yawancin su ‘yan tawaye ne.
Dama dai gwamnatin ta Myanmar tana daukar yan kabilar ta Rohingya a matsayin bakin haure ne daga kasar Bangaladesh, wadanda ba a taba basu takardan iznin zama ‘yan kasa ba duk da yake suna da iyaye da kakanninsu zaune a kasar shekara da shekaru.