Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Kunar Bakin Wake Kusa Da Ofishin Jakadancin Amurka A Kabul


Wani dan kunar bakin wake ya hallaka a kalla mutane 5 da kuma raunata wasu mutane 9 a wajen wani banki dake Kabul, babban birnin Afganistan.

An kai harinne a yau talata a kofar shiga bankin dake Kabul, wanda yake kusa da ofishin jakadancin Amurka mai matakan tsaro masu tsanani.

Shaidu sun bayyana cewa jami’an sojin Afganistan da sauran ma’aikatan tsaro na cikin jama’ar da suka taru wajan karbar albashinsu na wata a bankin.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin.

An kai mummunan harin yayinda kasar Afganistan ke shirye shiryen bukin Sallar Idi.

Mai Magana da yawun gwamnan lardin Herat, Jilani Farhad, ya fadawawa muryar Amurka cewa, harin da jirgin saman Amurka mara matuki ya kai ya hallaka a kalla farar hula 13, wanda ya hada da mata da kananan yara, ya kuma raunata wasu guda 7.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG