Hukumar kula da ‘yan Gudun Hijira ta kasa-da-kasa da ake kira IOM a takaice ta ce akalla mutane 18,000 ‘yan kabilar Rohingya suka gudu zuwa Bangladesh a cikin makon da ya gabata, tun lokacin da wani sabon fada ya barke tsakani wasu ‘yan bindiga da dakarun sojan kasar a makwabciyar ta, wato Myanmar.
Hukumar ta IOM ta ce wasu jerin hare-hare da wasu ‘yan bindiga Musulmi, ‘yan kabilar Rohingya suka kai akan dakarun tsaro a arewacin jihar Rakhine dake Myanmar, da kuma wasu fadace-fadace da suka faru daga baya, su suka haddasa wannan hijirar.
Hukumar ta kuma ce, mawuyacin abu ne a iya tantance adadin mutanen da suka makale a yanken dake kusa da iyakar kasar, koda yake kuma hukumar ta IOM ta ce mutanen da suka makale suna da yawan gaske.
Facebook Forum