A kasar India, akalla mutane 5 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa da guguwa suka haddasa a Mumbai, babban birnin kasar, a cewar jami’an gwamnati yau Laraba.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ya sa komai ya tsaya cik a birnin jiya Talata, wanda ya hana zirga-zirga a kan tituna kuma ya sa dole aka rufe tashoshin jiragen kasa da miliyoyin mutane ke amfani da su a yanken na dan lokaci. Dubban mutane sun makale a wuraren ayyukansu a daren jiya.
Sai dai jiragen sun cigaba da aiki sosai zuwa yammacin jiya Talata koda yake akwai cinkoso, kuma an rufe yawancin wuraren aiki da makarantu yau Laraba.
Birnin Mumbai dake kusa da gabar teku, mai yawan al’ummar da ta wuce miliyan 20, shine na baya-baya da ambaliyar ruwa ta shafa. A daminar bana mutane fiye da 1,200 suka mutu a kasashen India, da Nepal, da Bangladesh sakamakon ambaliyar ruwan.
Facebook Forum