Shugaban kungiyar kabilar Irigwe a karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato, Robert Ashi, ya tabbatar da mutuwar mutane hudu da kone gidaje fiye da dari da sare amfanin gona a wani sabon hari a karshen makon jiya.
Rikicin kablinacin a jihar ta Filato facce ke tsakiyar arewacin Najeriya ya Jima yana faruwa.
Sai dai a gefe guda kuwa shugaban kungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders a jihar, Nura Muhammad ya ce daga ranar Laraba zuwa ranar Asabar an kashe musu mutane Biyar da dabbobi.
A tafi aksarin lokuta, bangarorin biyu kan kai wa juna harin ramuwar gayya, zargin da sukan musanta.
Rundunar da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta ce ta yi namijin kokari wajen hana abin da ta ce taho mu gama tsakanin matasan Fulani da Irigwe.
Kwamandan rundunar, Manjo janar Ibrahim Sallau Ali a wata sanarwa ta hannun kakakin rundunar, Manjo Ishaku Takwa, ya ja hankalin masu ruwa da tsaki daga bangarorin Fulani da Irigwe kan su gargadi matasansu.
Matsalar tsaro a ‘yan kwanakin nan ya kazanta a kananan hukumomin dake arewacin a Filato abin da ya kai ga hukumomin cihar suka kaddamar da was Sabin kayan aiki a 'yan makonnin baya.
Gwamna Simon Lalong ya ce dalilin samar da kayayyakin da suka hada da motoci da basura shi ne, don a magance hare-haren da ake kai wa a sassan jihar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5