Wasu ‘yan bindiga sun hallaka makiyaya bakwai a kauyen Dogon-Gaba dake karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato a tsakiyar arewacin Najeriya.
Mahaifin daya daga cikin wadanda aka kashen, Ibrahim Makaho ya ce maharan sun fito ne ta yankin Kwall a karamar hukumar Bassa, a wata mota kirar J5.
“Kamar wadanda suka gani suka shaida mana, sun z da J5 suka tsaya a daidai wnai kauye Danda, yaranmu suna kiwo a wurin ba san komai ba, suka biyo su har wani kauye da ake cewa dogon gaba, anan suka kashe yara guda bakwai, aka kashe shanu aka tura wasu aka tafi da su.” In ji Ibrahim Makaho.
Kai wa juna hari da ramakon gayya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kananan hukumomin arewacin jihar Filato ya kasance barazana ga zaman lafiya a yankin.
Kakakin kungiyar kabilar Irigwe, wadanda makiyayan ke dora alhakin kisan akansu, Davidson Malison ya ce ba su da labari kisan.
“Gaskiya yanzu nake ji daga wurinki…. gakisya ban san da wani abu haka ba, kuma ina ganin mutanenmu ba su yi wani abu haka ba.” In ji Malison.
Shugaban kungiyar hadaddiyar kungiyoyin matasan Fulani a Najeriya, Abdulkarim Bayero yayi kiran da akai zuciya nesa.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa a jihar Filato, Mr. Dan Manjang ya ce a kwanannan gwamnati ta sayo motoci da sauran na’urorin tsaro ta kuma horadda matasa dubu uku a dukkan kananan hukumomin jihar wadanda za su taimaka wa jami’an tsaro da bayanai.