A Janhuriyar Nijar,Jam'iyyar adawa ta MNSD NASARA ta zargi jam'iyyar PNDS TARAYYA da haddasa rikici a bangaren adawa.
WASHINGTON, DC —
Batun shiga gwamnati ya janyo rigima a bangaren siyasar Janhuriyar Nijar, inda jam'iyyar adawa ta MNSD NASARA ke zargin jam'iyyar PNDS TARAYYA da haddasa mata rikici da sunan goron gayyatar shiga gwamnatin rikon kwarya.
Wakilinmu a Nijar Abdullahi Mamman Ahmadu ya ce Mataimakin Shugaban Jam'iyyar MNSD na kasa shiyyar Doso kuma kakakinta, Alhaji Hamma Zada ya ce shiga gwamnati da wasu 'yan jam'iyyar su shida su ka yi wata gadar zare ce aka shirya wa bangaren adawa.
To amma Shugaban Riko na PNDS TARAYYA kuma Ministan Harkokin Wajen Nijar, Malam Bazu Mohammed nemi 'yan jam'iyyar adawa ta MNSD da su fahimci cewa rashin jagoranci na gari ne kan haddasa tsattsaguwa tsakanin 'yan jam'iyya.
Rikicin Siyasar Nijar