A makon jiya ma, sai da firayim ministan Nijar din ya tuntubi kotun tsarin mulki ta kasa a kan ko 'yan adawa su na iya shiga cikin gwamnatin hadin gambiza ta kasa ba tare da sun saba tsarin mulkin kasar ba. Kotun ta ba shi amsa da cewa, jam'iyyun adawa su na iya shiga cikin gwamnati a dama da su.
Wani kakakin gamayyar jam'iyyun adawar a Nijar, Alhaji Doudou Rahama, yace su na iya shiga cikin gwamnatin idan har shugaban kasa zai cika sharrudan da suka gindaya. Yace yin hakan ba zai nkawar da nauyin dake wuyansu na kare muradun 'yan kasa da tabbatar da cewa gwamnati tana aiki ma jama'a ba.
'Ya'yan jam'iyyar PNDS-Tarayya dake mulkin kasar, sun yaba da abinda suka bayyana a zaman hangen nesa na shugaba Mahamadou Issoufou wajen gayyato 'yan adawa cikin gwamnatinsa. Memba na jam'iyyar, Alhaji Asoumana Muhammadou, yace shigar da 'yan hamayyar zata kawar da irin rigingimun da aka yi ta gani cikin gwamnatocin kasar da aka yi shekaru 20 da suka shige.
Ga cikakken bayanin da wakilin sashen Hausa, Abdoulaye Mamane Ahmadou, ya aiko daga birnin Yamai.