Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gaisuwar Shugaban Gidan Rediyon Muryar Amurka Ga Al'ummar Musulmin Duniya


Shugaban Gidan Rediyon Muryar Amurka David Ensor, ya yi wa Musulmin Duniya barka da shan ruwa.
Shugaban Gidan Rediyon Muryar Amurka David Ensor, ya yi wa Musulmin Duniya barka da shan ruwa.

Shugaban Gidan Rediyon Muryar Amurka, David Ensor, ya yi wa Musulmin Duniya Barka

A sa'ilinda ake bukukuwan Sallar "Eid el Fitr" wato karamar Salla, ko Sallar Idi a Janhuriyar Nijar; ake kuma harmar Sallar a sauran kasashen duniya, Shugaban Gidan Rediyon Muryar Amurka, David Ensor, ya yi wa al'ummar Musulmin duniya barka da kammala azumin watan Ramadan.

David Ensor ya ce: "Salama'alaikum, ni ne David Ensor, Daraktan Gidan Rediyon Muryar Amurka a Washington DC. A madadin dukkannin ma'aikatan Gidan Rediyon nan na Muryar Amurka, ina son yi wa Musulmi masu kallo da saurara nmu fatan 'Eid el Mubarak.'

A lokacin wannan wata mai alfarma na azumin Ramadana ma'aikatanmu sun yi ta kawo ma ku labarai iri-iri daga sassan duniya daban-daban, musamman ma kan yadda Musulmi a ko'ina a duniyar nan su ke gudanar da hidimomin wannan wata mai alfarma na Ramadan. Mu na fatan cewa wannan aikin na mu na kawo ma ku labarai da bayanai zai dada inganta kusancinmu da dangantakarmu da juna a wannan lokaci na sabunta zumunci da cude-ni-in-cude-ka tsakanin al'ummomi. Mu na kara gode ma ku da kasancewa tare da Gidan Rediyon Muryar Amurka.

Wassalamu'alaikum.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG