Ganin irin wannan matsala da kasar take fuskanta, da kuma ganin cewa ita kanta tana samar da bakin hauren dake kokarin satar shiga kasashen na Turai, ya sa hukumomin kasar tare da hadin kan Kungiyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, da kuma kasar Spain, zasu kaddamar da wani sabon shirin dakile kwararar irin wadannan bakin haure.
Shirin da zai ci kudi mai dan karen yawa, zai shafi horas da jami'an tsaro da dogarawan bakin iyaka, tare da samar musu da kayan aiki na zamani ta yadda zasu iya tarewa da juya akalar irin wadannan bakin hauren.
Za a shafe tsawon watanni 18, ko shekara daya da rabi, ana aza harsashin wannan sabon shirin wanda ba kawai zai ma dakile irin bakin hauren dake bi ta cikin kasar ba ne, zai kara karfafa tsaron bakin iyaka da kuma kasar ta Nijar baki daya.
Wakilin sashen Hausa, Abdoulaye Mamane Ahmadou, ya aiko mana da karin bayani daga Yamai.