Rahotanni daga jahar Taraba na nuna cewa sakamakon zaben gwamnan jahar ya kawo takaddama inda wasu matasa suka fusata kuma suka kona gidan sakataren gwamnati jahar da na dan majalisar da kuma hallaka mutane uku.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana a rahoton, takaddamar ta taso ne a yankin Gyembu a sakomakon fadin cewar jam'iyar APC ce ta lashe zabe sannan aka koma aka sake cewa jam'iyar PDP ce ta yi nasara a wasu kananan hukumomin jahar.
A cewar kakin rundunar 'yansandar jahar Taraba ASP Mr Joseph Kaje yace bai tabbatar da aukuwar hakan ba amma suna kan bincike.
Jam'iyar APC ta bakin shugaban jam'iyar Alhaji Hassan Hardo tayi fatali da sakamakon zaben da take ganin ana anfani da jami'an tsaro wajan yin yadda aka ga dama kamar su kwace akwatunan zaben da sauransun su, haka kuma jam'iyar PDP ta bakin shugaban nata Hon, Victor Bala Kona ya musanta abin domin a cewar sa jama'a na ra'ayin jam'iyar su ne shiyasa suke a kan hanyar lashe zaben.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Attiki abubakar ya nuna cewar babu shakka suna sa ran zasu lashe zaben jahar ta Taraba.
Your browser doesn’t support HTML5