Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamiyyar APC Tayi Nasarar Lashe Zaben Gwamna a Jihar Neja


MATA SUNA LAYIN ZABE
MATA SUNA LAYIN ZABE

Hukumar zaben Najeriya ta sanar da sakamakon zaben jihar Neja, baturen zaben Farfesa Bature Hambali yace sun gama hada hancin zaben.

Hukumar zaben Najeriya ta sanar da sakamakon zaben jihar Neja, baturen zaben Farfesa Abdulganiyu Hambali yace sun gama hada hancin kuriaar da aka kada a zaben gwamnan daga kananan hukumomi 25 dake fadin jihar Neja, sannan ya bayyana cewa.

''Abubaka Sani Bello na jamiyyar APC ya samu kuriu dubu dari biyar da casain da ukku da dari bakwai da biyu (593,702) Umar Mohammed Nasko na jamiyyar PDP ya samu kuriu dubu dari biyu da talatin da tara da dari bakwai da sabain da biyu (239,772)''

Shugaban hukumar zaben yaci gaba bayani kamar haka.

''Abubakar Sani Bello bayan ya cika duka sharuddan da doka ta tanada kuma ya samu kuriu mafi rinjaye don haka shine wanda yayi nasara a wannan zabe''

Tuni Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayyana farin ciki akan nasarar da ya samu, sailin nan ya nemi masu taya shi murna da suyi a hankali.

''Ina fata ko za ayoi biki na murna ayi a hankali sabo da wancan karon anyi kuma an samu hatsarurruka da yawa, har wau sun rasa rayukan su, dan haka a samu dan natsuwa ayi nishadi cikin hikima''

Jamiyyar PDP dai data sha kayi ta rungumi kaddara Barister Tanko Beji shine mataimakin shugaban jamiyyar ta PDP a jihar Neja.

''Wanda ALLAH yaba ALLAH taya shi riko, ALLAH yasa ace gara da akayi ita mulki ai haka take.

Ga Mustafa Nasir Batsari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:05 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG