Bayan an yi watanniana ta jita-jita tsohuwar tsohuwar sanata kuma tsohuwar sakatariyar harkokin waje Amurka Hillary Clinton ta fito ta a hukunce bayyana cewar zata tsaya takarar shugaban kasa na shekara mai zuwa idan Allah ya kaimu.
Tace kullu yaumi Amerikawa suna bukatar shugaba na gari, kuma tace tana son zama wannan shugaba domin baku damar yin sauran abubuwan cigaban rayuwan. zai sa ku cigaba kuma ku zauna a gaban. Amurkawa sunyi fifutika daga matsalar tattalin arziki. Amma har yanzu na sama ne ke cin moriya.”
Hillary Clinton dai itace ‘yar jam’iyyar Democrat ta farko data ta bayyana aniyar tsayawa takara domin maye gurbin shugaba Obama, wanda ya kada ita a zaben firamare na shekara ta 2008.
A wani zabe da akayi na jin ra’ayin jama’a bada dadewa ba na nunin Clinton ce gaba da sauran mutanen da ake tsammanin zasu tsaya takarar a jam’iyyar Democrat. Ana kuma ganin itace zata lashe zaben na shekara ta 2016 kan duk ‘yan takarar jam’iyyar hamayya ta Republican.