A yayin da ake cigaba da tattarawa da kuma bayyana sakamakon zaben Gwamnoni da na ‘yan majalisu a sassa daban daban a Najeriya, wakiliyar sashin Hausa Zainab Babaji ta aiko mana da rahoton da ke kumshe da sakamakon zaben jahar Filato.
Jami’in tattara kuri’u na hukumar zaben jahar Filato kuma shugaban jami;ar harkokin noma dake jahar Benue farfesa Emanuel Kuca, ya bayyan sakamakon zaben cewa.
Jam’iyar APC nada kuri’u 564,913. Sai kuma jam’iyar PDP mai kuri’u 520,627. Jami’in ya kuma Aiyana Simon Lalong na jam’iyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben inda ya doke abokin takarar sa sanata Gyang Yom Shang Pwajok na jam;iyar PDP.
Idan muka koma jahar Nasarawa kuma, gwamna mai ci Ummaru Tanko Alma’kura na jam’iyar APC ne ya lashe zaben da kuri’u 309,746. inda ya doke abokin takarar sa Labaran Maku na jam’iyar APGA wanda ke da kuri’u 178,983.
Shikuma dan takarar gwamnan jahar ta Nasarawa Yusuf Agabi, yazo na uku ne da kuri’u 119’782 kamar yadda jami’in tattara sakamakon zaben jahar Nasarawa, kuma shugaban jami’ar tarayya dake Lokja farfesa Hassan Rafin Dadi ya bayyana.
Haka kuma jahar Benue, jami’in tattara kuri’un kuma shugaban jami’ar Jos farfesa Heward Babale Mafuwai ne ya bayyana Samuel Otom na jam’iyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 422,932. Inda ya doke abokin takarar san a jam’iyar PDP Tehemen Tazur wanda keda kuri’u 313,878.
A yanzu haka dai jam’iyar APC ce ta lashe zabe a jahohin Filato, Nasarawa da Benue dake dake shiyar arewa ta tsakiyar Najeriya.