Rawar Da Rundunar Sojojin Ruwan Najeriya Ke Takawa Wajen Samar Da Tsaro

Mayakan Ruwa suna hallartar taron sauyin shugabanci a birnin Abuja Junairu 20, 2014.

Rundunar sojojin ruwan Najeriya sun gudanar da sintirin awa 22,000 cikin shirin samar da tsaro a kasar ta cikin ruwa.

Babban hafsan hafsoshin rundunar sojojin ruwan Najeriya,Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe, ya ce shirin sintirin samar da tsaro mai taken Operation Tsare Teku da Operation River Sweep, wasu sintiri ne da a halin yanzu suke gudana don samar da tsaro.

Ya ci gaba da cewa duk kuwa da kalubalen da ake fuskanta sojojin ruwan Najeriya na samun kwarin gwiwa da kuzari sosai bisa irin nasarar da suka samu yanzu.

Cikin shekarar da ta gabata rundunar sojin ruwan Najeriya sun yi sintiri na kimanin awa 22,000 inda aka cafke ‘yan ta’adda 42, wadanda a halin yanzu ke fuskantar bincike da shari’a a kotuna daban-daban.

Masanin tsaro, Kwamarad Abubakar Abdussalam, ya tabbatar da nasarar da sojin ruwa ke samu a ayyukan da suke gudanarwa.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Rawar Da Rundunar Sojan Ruwan Najeriya Ke Takawa Wajen Samar Da Tsaro - 2'10"