Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce yaki da cin hanci da rashawa ba zai samu cin nasara ba sai an dawo da kudaden Afirka da aka sace a ka boye a bankunan kasashen waje.
Farfessa Osinbanjo yace a duk shekara Afirka na hasarar dalar Amurka biliyan hamsin sanadiyyar cin hanci da rashawa. Farfesa Osinbajo yana magana ne a taron hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afirka wadanda da Birtaniya ta yiwa mulkin mallaka, da aka yi a Abuja.
Mataimakin shugaban Najeriyan ya ce ya zama wajibi kowa ya yi anfani da kudin da aka dawo dasu domin anfanin al'ummar kasashensu yadda ya dace.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasar Namibia ya ce, akan mayar da jami'an hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa saniyar ware a cikin al'ummarsu. Yana fargabar zasu iya rasa rayukansu, amma duk da haka ba zasu yi kasa a gwuiwa ba.
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya ce a zamanin su babu irin wannan illar, duk da haka ya bada shawarar a inganta albashin ma'aikata domin hana su karkatar da kudaden gwamnati.
A cewar Janar Gowon, a lokacin dukansu suna tsoron Allah tare da yin alkawarin ba zasu zambaci mutanen Najeriya ba.
Tsohuwar shugabar hukumar yaki da cin hanci da rsahawa ta Najeriya EFCC, Farida Waziri, ta nanata matakin da taso ta dauka na cewa a binciki kwakwalwar masu aikata almundahana.Ta ce abun yana bata mamaki yadda wani zai saci kudi ya je Amurka da wasu kasashen duniya ya sayi gidaje sannan ya ce shi ya saka jari. Ta ce irin wannan bashi da kai saboda 'yanuwan shi ko ruwan sha basu dashi.
Mukaddashin hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Najeriya Ibrahim Magu, ya ce ba'a fara ganin irin dirar mikiya da hukumarsa zata yi akan wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa ba.
Hukumar ta Najeriya ta nuna hotunan mutanen da take zargi da yin zarmiya da 'yan damfara da kuma masu kera dala ta jabu har da bokaye dake taimakawa barayi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum