Al’ummar yankin Ugya dake karamar hukumar Toto dake jihar Nasarawa sun bukaci gwamnatocin tarayya da na jiha da su ziyarci yankin domin kawo karshen kashe kashen dake ake yi tsakanin kabilun Ebira da Bassa.
Tun a watan jiya ne al’ummomin yankin na Ugya da kewaye suka samu kansu a cikin wani rikicin da ya samo asali daga jihar Kogi ya shigo jihar Nasarawa.
An samu asarar rayuka da dama da raba wasu da muhallansu.
Malam Dansabo Friday wanda yake magana da yawun kabilar Bassa, yace har yanzu ana ci gaba da kisshe mutane kuma babu jami’an tsaro a yankin. Kawo yanzu sun ga gawarwaki 31 tare da bacewar wasu da basu san inda suke ba. Ya roki gwamnan jihar Nasarawa ya je Ugya.
Akwai sojoji a garuruwan Toto da Umaisha, amma inda ake kashe kashen babu soja ko daya. Ya roki gwamnan jihar ya kafa kwamitin da zai kunshi mutanen kabilun biyu domin zakulo bakin zaren warware matsalar
Friday ya kuma bukaci a samar wa wadanda suka rasa gidajensu, matsuguni na wucin gadi tare da nanata cewa, rikicin bana addini ba ne. Yace duk wanda y ace rikicin addini ne, yayi karya.
Wani mutum mai suna Jaafaru na al’ummar Bassa ya nemi a yi hakuri da juna a nemi yin sulhu.
Shi ko gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura y ace suna sane da abun dake faruwa a yankin saboda haka ne suka tura jami’an tsaro. A cewarsa al’ummomin Bassa da Ebira da suka fito daga Kogi suna zuwa wurin ‘yan uwancu a cikin jihar Nasarawa suna ruruta wutar tashin hankali ta yin anfani da abun da ya faru kimanin shekaru 18 da suka wuce.
Yanzu ma sun koma yakin sari ka noke ne a yankin, suna kone gidaje da sace mutane. Gwamna Tanko Al-Makura yace sun girka jami’an tsaro a yankin, kuma duk wanda aka kama da makami kowane iri ne sai an tabbatar bai yiwa kowa wani abu ba.
Gwamnan ya yi alkawarin zuwa yankin mako mai zuwa inda ya yiwa kabilun biyu nasiha, da gargadi tare da kuma baiyana masu abun da gwamnati keyi domin tabbatar da zaman lafiya.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani
Facebook Forum