Masarautar Kontagora dake jihar Neja ta dauki matakin sanya idanu akan duk wasu baki masu shiga yankin domin tabbatar da tsaro.
A wani babban taron shekara-shekara da aka gudanar a masarautar, mahalarta taron sun yi tsokaci akan muhimmancin zaman lafiya da neman ilimin zamani dana Muhammadiya, sannan da fadakar da matasa akan illar shiga bangar siyasa.
A cikin jawabin da ya gabatar Mai Martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Saidu Namaska, wanda madawakin Kontagora Alhaji Aminu Madawaki ya wakilta, ya umurci hakimai da masu unguwanni na masarautar, da su sanya idanu sosai, musamman ga 'yan gudun hijira dake kwararowa cikin yankin sakamakon tashin hankalin jihar Zamfara da na yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna.
A nashi bangaren tsohon gwamnan jihar Kano Kanar Sani Bello mai ritaya, yayi kira da a kaucewa tashin hankali irin na siyasa, saboda idan babu zaman lafiya babu abun da za'a iya yi hatta irin wannan taron da su keyi. Ya kara da cewa mazauna yankin su dauki darasi daga wadanda rikici ya raba su da muhallansu da matansu da 'ya'yansu. Ya ce a yi kokari a zauna lafiya.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana muhimmancin wayar da kawunan jama'a akan addinin musulunci da kuma neman ilimin zamani.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum