Rasuwar Lagbaja:Tinubu Ya Bada Umarnin A Yi Kasa-Kasa Da Tutocin Najeriya

Laftanar Janaral Taoreed Abiodun Lagbaja

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bada makamancin wannan umarni a sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Muyiwa Adejobi ya fitar.

Sakamakon rasuwar babban hafsan sojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, gwmnatin tarayya ta bada umarnin sauke tutoci kasa-kasa a fadin kasar tsawon kwanaki 7 domin nuna girmamawa ga marigayin.

A sanarwar daya fitar a jiya Laraba, ta hannun daraktansa na yada labarai da hulda da jama’a, Segun Imohiosen, Sakataren Gwamnatin Tarayya, yace shugaban kasa ya bada umarnin sauke tutocin Najeriya kasa-kasa a fadin kasar tsawon kwanaki 7 domin karrama marigayi babban hafsan sojin kasan, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Ya kuma yabawa irin sadaukarwar da marigayin ya yiwa Najeriya sannan ya yi fatan Allah ya baiwa iyalansa juriyar wannan babban rashi.

Shima, Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bada makamancin wannan umarni a sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Muyiwa Adejobi ya fitar.

Jami’an ‘yan sanda zau rika daura bakar kambi a hannunsu tsawon kwanaki 7 domin girmama marigayi babban hafsan mayakan kasan Najeriya

Babban sufeton ‘yan sandan ya bada umarnin ne a cikin sanarwar da kakakin rundunar Muyiwa Adejobi ya fitar.

"Bayan rasuwar babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban sufeton ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bukaci yansandan su ɗaura bakin kambi a hannu na tsawon kwana 7 domin jimamin rasuwar babban hafsan.

“An bayar da umarnin ne domin alhini da girmamawa kan irin sadaukarwa da jajircewa da yaki da miyagun laifuka da ya yi. Shi din babban jagora ne da ya dace da girmamawa ta ko'ina'', a cewar Adejobi

Babban hafsan mayakan kasan Najeriyar ya rasu ne a Talatar data gabata, a cewar fadar shugaban kasar.

Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya rasu ne a Legas bayan ya sha fama da jinya. Sai dai, ba’a bayyana kowace irin jinya ba ce.