Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Cewa A Yi Juyin Mulki Suna Cin Amanar Kasa – Hedkwatar Tsaron Najeriya


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

“Hedkwatar tsaron Najeriya na so ta fayyace cewa ba ta nada wani mukaddashin Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke cewa."

Hedkwatar Tsaron Najeriya ta yi gargadi ga masu kiraye-kirayen a yi juyin mulki a kasar inda ta kwatanta lamarin a matsayin cin amanar kasa.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, hedkwatar tsaron ta Najeriya ta kuma musanta rahotanni da ke cewa an nada mukaddashin Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya.

“Wadanda ke kira a yi juyin mulki kamar yadda ake gani a fina-finan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta, su kwan da sanin cewa yin hakan laifi ne na cin amanar kasa karkashin kundin tsarin mulki.” Sanarwar dauke da sa hannun Darektan yada labarai Birgediya Janar Tukur Gusau ta ce.

Sanarwar har ila yau ta ce rahotannin da ke cewa an nada mukaddashin Babban Hafsan Sojin kasa babu gaskiya a cikinsu.

“Hedkwatar tsaron Najeriya na so ta fayyace cewa ba ta nada wani mukaddashin Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke cewa.

“Babban Hafsan Sojin kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya tafi hutun shekara ne. Manjo Janar AbdulSalam Bagudu Ibrahim wanda shi ne shugaban tsare-tsare na kai wa Janar Lagbaja rahotanni kamar yadda tsarin aikin soja ya tanada.” In ji Janar Tukur.

A karshen makon da ya gabata aka samu rahotannin da ke cewa Janar Lagbaja ya rasu bayan fama da cutar daji, rahotannin da rundunar sojin kasar ta musanta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG