Babban dajin Birnin Gwari da ya hada yankunan jihohi uku na Kaduna, Naija da Zamfara a Arewacin Najeriya, yana daga cikin wuraren da ake noma kaso mafi tsoka na kayan abinci a yankin.
To sai dai tawon shekaru ke nan manoma a yankin ba sa samun sukunin yin noma, sakamakon mamayewar da ‘yan bindiga suka yi a wajen.
Hasali ma kauyuka da dama sun tashi daga yankin, saboda ayukan ‘yan bindigar, da suka hada da kai hare-hare, satar shanu da kuma satar mutane domin karbar kudin fansa, wanda ya zama ruwan dare a yankin.
Yanzu haka ana tunkarar saukar damina, amma babu alamun wani shirye-shiryen soma kimtsawa aikin gona a yankunan na dajin Birnin Gwari da kewaye kamar yadda aka al’adanta, na share gona, kai taki da dai sauransu.
Mai sharhi kan lamurran yau da kullum kuma Dan-masanin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Idris Abdurra'uf ya ce bana ma dai lamarin ya ta'azzara, saboda sharudda masu tsaurin gaske da 'yan bindigar su ka shinfidawa manoma.
Ya ce ”yanzu dai aikin gona ya gagara a yankin Birnin Gwari duk kuwa da bukatar da manoman ke da ita na zuwa gona don soma shirye-shirye da hako arzikin albarkatun noma a yankin.
Wannan matsala dai ta dade ta na ci wa mahukuntan Najeriya tuwo a kwarya, kamar yadda kwamishinan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyanawa manema labarai, bayan tashi daga wani taro kan sha’anin tsaro a Kaduna, inda ya ce duk da nasarorin da jami'an tsaro ke samu kan 'yan bindiga, har yanzu akwai kalubalen tsaro.
To sai duk da ta'azzarar wannan matsalar ta tsaro, Dan masanin Birnin Gwari, na ganin akwai mafita idan aka sauya salo.
Ya ce “sai an yi da gaske. Jami’an tsaro suna iya kokarinsu. Amma maganar nan da nake da kai, tsakanin Manina da Mariga ‘yan bindiga na cin karensu ba babbaka. Kullum suna harbe na harbewa, su raunata wasu, sannan su kwashi wasu mutane a shiga da su daji domin karbar kudin fansa.”
“Saboda haka dole jami’an tsaro su sauya salo kuma su kara kaimi, sannan a sami wadanda za su taimaka musu a shiga cikin wadannan dazukan, domin duk abin da aka yi kan hanya idan ba’a shiga dazukan ba, to ba yadda za’a yi a kawo karshen wannan matsala.”
Wannan dai ba shine karon farko da 'yan-bindiga ke shinfidawa manoma sharuddan zuwa gonakin su ba, sai dai kuma manazarta na ganin saka ka'idojin tun kafin sharar gona alama ce ta sauya salon da ke bukatar mahukunta su dauki mataki tun kafin abin ya gagari kundila.
Cikakken sautin rahoton Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5