Galibi dai matsalar tsaro yayin gudanar da zabubbuka a Najeriya ba
wani sabon abu ba ne, to amma irin salon da hakan ya dauka yayin sake
gudanar da zaben gwamna a jihar Adamawa al'amari ne da kwararru a
fannonin tsaro da sha'anin siyasa ke cewa na da daure kai, musamman
ganin yadda wasu 'yan dabar siyasa suka afkawa wani babban jami'in
hukumar tsaron farin kaya da ma wani kwamishinan tarayya na hukumar
zabe ta kasa, to shin me ke jawo hakan, kuma menene maganin afkuwar
irin haka nan gaba? Tambayar kenan da shirin na wannan mako zai kokarin amsawa.