Rashford Ya Yi Hatsarin Mota

Rashford

Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta, sun nuna motar ta Rashford ta lalace.

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford ya yi hatsarin mota a ranar Asabar.

Hatsarin ya auku ne yayin da yake barin filin atisaye a ranar Asabar a motarsa kirar Rolls Royce a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP.

Kamfanin Dillancin labaran Birtaniya na PA, ya ruwaito cewa hatsarin ya faru ne bayan da United ta dawo filin atisayenta da ke Carrington bayan doke Burnley da ci 1-0 a gasar Premier League.

Bayanai sun yi nuni da cewa, ‘yan wasan United sun bi motar bas din kungiyar wacce ta ajiye su a filin atisayen don kowa ya dauki motarsa ya kama hanyar gida.

A hanyarsa ta komawa gida hatsarin ya faru.

Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta, sun nuna motar ta Rashford ta lalace.

Sai dai dan wasan bai ji ko kwarzane ba, kamar yadda ya tabbatar a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi.

“Ina cikin koshin lafiya, na gode da sakonninku.”