Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Na Zawarcin Neymar


Neymar
Neymar

Kwantiragin Neymar zai kare a shekarar 2025, yana kuma da zabin tsawaita shi zuwa 2027.

Kungiyar Manchester United ta Ingila, na bibiyar dan wasan PSG Neymar, gabanin a bude kasuwar ‘yan wasa a lokacin bazara.

Ana hasashen Neymar, wanda dan asalin Brazil ne zai bar PSG a karshen kakar wasan nan da ke shirin karewa, ya koma kungiyar ta Red Devils in ji jaridar Foot Mercato.

Baya ga United, kungiyar Chelsea ma na bibiyar dan wasan, kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Kwantiragin Neymar zai kare a shekarar 2025, yana kuma da zabin tsawaita shi zuwa 2027.

Amma wasu rahotanni na cewa kungiyar ta PSG na da burin rabuwa da dan wasan, duk da cewa yana da sha’awar ci gaba da zama a kungiyar ta PSG da ke Faransa.

Wannan ba shi ne karon farko da kungiyar ta United take nuna sha’awar sayen dan wasan ba, a shekarun baya ta yunkuri da dama wajen sayen shi, amma abin ya ci tura.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG