Rasha Ta Harba Makamai Masu Linzami Daka Iya Yin Dakon Nukiliya Cikin Ukraine

Makami Mai Linzami

Kasar Rasha ta harba makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa birnin Dnipro na Ukraine a yau Alhamis, a cewar rundunar mayakan saman birnin Kyiv, a wani al’amari da za’a iya kira da karon farko na yin amafani da makaman da aka kera domin kai harin nukiliya zuwa nesa.

Harin, idan ya tabbata, na bayyana karuwar tashin hankali cikin sauri a yakin da aka shafi watanne 33 ana gwabzawa bayan da Ukraine ta harba makamai masu linzami kerar Amurka da Burtaniya zuwa cikin Rasha a makon da muke ciki duk da gargadin da Moscow ta yi na cewar za ta kalli hakan ne a matsayin babbar tsokana.

Masana harkokin tsaro sun ce wannan na iya zama karon farko da aka yi amfani da irin wadannan makamai masu cin dogon zango daka iya daukar nukiliya (ICBM). An tsara irin wadannan makamai na ICBM ne domin kai harin nukiliya kuma wasu muhimman bangare ne na rigakafin da Rasha keda shi akan nukiliyar.

“A yau an ga sabon makamin Rasha mai linzami. Dukkanin siffofinsa sun cika - kama daga hanzari zuwa irin rimin da ya yi - dukkaninsu na makamin ICBM mai daukar nukiliya ne. Kwararru na ci gaba da bincike akai,” kamar yadda shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana a sanarwar da ya fitar ta faifan bidiyo.

Rundunar sojin saman Ukraine tace an harba makamin ne daga yankin Astrakhan na Rasha, nisan fiye da kilomita 700 daga Dnipro dake shiyar tsakiya maso gabashin Ukraine. Bata fayyace abin da makamin ke dauke da shi ba ko ma wani irin samfurin makami mai linzami ne shi.

Sai dai babu abin da ke nuna cewar makamin na dauke da nukiliya.

-Reuters