Rasha Ta Fara Aiwatar da Shirin Tsagaita Wuta A Syria Domin Aikin Jinkai

Barin wutar jiya ta haddasa mugun hayaki tare da hallaka akalla mutane shida

Shugaban Rasha Vladimir Putin ne ya ba da umurnin tsagaita wutar amma wannan bai hana mutuwar mutane shida ba yau sanadiyar barin wutar da dakarun gwamnatin Syria din suka dinga yi akan 'yan tawaye

Rasha ta fara aiwatar da shirinta na "tsagaita wuta domin a gudanar da ayyukan jinkai" a yankin Ghouta na kasar Syria a jiya Talata, amma wani sabon fada ya kaure a yankin, kana kuma babu alamar farin kaya na ficewa daga yankin da aka kewaye ko isar kayayyakin jinkan.


A kalla farin kaya guda shida aka kashe a cikin wuni guda da Rasha ta tsagaita wuta, bisa umarnin da shugaba Vladmir Putin ya bayar na dakatar da kai farmaki a yankin dake hannun 'yan tawaye kuma a ba farin kaya damar ficewa daga yankin mai fama da tashin hankali dake kusa da babban birnin Syria, Damascus.


Babu wani farin kaya da aka ga yana ficewa a wani shingen da gwamnatin Syria ta kafa a yankin da ake gwabza yakin, wani wurin da aka ajiye hotunan Putin da shugaban Syria Bashar al-Assad a kusa da juna.